Labarai
Ranar abinci ta duniya : Najeriya ce ta 98 a kasashen duniya dake fama da Yunwa
Kungiyar masana kimiyyar abinci mai gina jiki ta kasa ta ce Najeriya ce ta 98 a cikin jerin kasashen duniya 107 da al’ummarta ke fama da yunwa sakamakon, rashin abinci mai gina jiki.
Shugaban kungiyar reshan jihar Kano Auwal Musa ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio, wanda aka tattauna kan ranar abinci ta duniya da ake gudanarwa a yau.
A cewarsa hakan na faruwa sakamakon karancin wayewa da al’ummar ke fama ita, wajen sanin abinda ya kamata su noma da zai wadatar da al’umma.
A na ta bangaren mataimakiyar shugaban Sa’adatu Sulaiman, ta bayyana cewar wannan matsala da ake fuskanta ta yunwa a kasa, tana da nasaba ne da yadda manoman kasar nan ba sa samun ingantattun kayan aiki.
Bakin da aka tattauna da su a cikin shirin sun bukaci hukumomi da su kara kaimi wajen inganta fannin kiwon lafiya, musamman ma samar abinci mai gina jiki ga al’ummar kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login