Labarai
Ranar Hausa: Ƙasashen duniya na ci gaba da karɓar harshen Hausa – Ƙungiya
Ƙungiyar Hausawan Afrika ta ce, harshen Hausa na ci gaba da samun ɗaukaka a kasashen duniya la’akari da yadda yake samun masu koyan sa.
Wakilin kungiyar reshen jihar kano Alhaji Ado Gambo Ja’een ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan ranar Hausa da take gabatowa.
Alhaji Ado ya ce, tasirin harshen ya kai har wasu ƙasashen duniya na ƙoƙarin koyan sa da kuma al’adun sa.
Alhaji Ado ya bayyana damuwar sa kan yadda harshen ne kawai ke samun ɗaukaka, amma al’adun sa a kullum suna samun koma baya.
You must be logged in to post a comment Login