Labarai
Ranar kare haƙƙin ɗan adam: Muna fuskantar ƙalubale na janyewar waɗanda aka takewa haƙƙi adaidai lokacin da ake gab da samun nasara a kotu – Shafi’u Yakasai
Kungiyar da ke ranjin kare haƙƙin ɗan adam a Kano ta Human Right Network ta ce, babban ƙalubalen da take fuskanta shi ne janyewar waɗanda aka takewa haƙƙi adaidai lokacin da ake gab da cin nasara a gaban kotu.
Sakataren mulki na kungiyar kwamared Shafi’u Wada Yakasai ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na freedom Radio.
“Ƙungiya na iya ƙoƙarinta wajen ganin an hukunta waɗanda aka kama da yiwa ƙananan yara fyaɗe ko safararsu ko kuma bautar da su, sai dai wadanda abin ya shafa kan daykile mu ta hanyar janye ƙarar”.
“Ana dannewa mutane haƙƙinsu ba tare da sun sani ba hakan yasa muke shirya taron gangami da maƙaloli a kwanaki 10 na farkon watan Disamba domin wayar da kan mutane su san ƴancinsu.
Majalisar ɗinkin duniya ce dai ta ware ranar 10 ga Disamba domin wayar da kan mutane don su san haƙƙinsu na ɗan adam.
A bana an yiwa ranar ta ke da “Samar da daidaito” da nufin magance matsalolin wariyar launin fata da ƙyama da kuma take haƙƙin ɗan adam.
You must be logged in to post a comment Login