Connect with us

Ƙetare

Rasha ta kai mummunan hari kan lantarkin Ukraine

Published

on

Hukumomin kula da lantarki a Ukraine sun bayyana cewa rundunar sojin Rasha ta kai wani mummunan hari kan manyan cibiyoyin samar da wutar lantarki a fadin kasar, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a jihohi da dama. Kamfanin kula da lantarki na kasar, Ukrenergo, ya ce harin ya faru ne a safiyar Asabar yayin da ake ci gaba da yakin da ya shafe kusan shekaru hudu ana yi tsakanin kasashen biyu.

 

Jami’an Ukraine sun zargi Rasha da kai hare-hare kai tsaye kan kayayyakin more rayuwa, musamman wutar lantarki, lamarin da ya jefa daruruwan dubban mutane cikin duhu da sanyi, musamman a wannan lokaci da yanayin sanyi ya tsananta ƙwarai. Ukrenergo ta ce an dauki matakan gaggawa na katse wuta a yawancin yankunan kasar sakamakon barnar da harin ya haifar.

 

Duk da ci gaba da wadannan hare-hare, Ukraine da Rasha sun gudanar da tattaunawa biyu karkashin sasancin Amurka a birnin Abu Dhabi tun daga watan Janairu. Duk da cimma matsaya kan musayar fursunoni, bangarorin biyu sun kasa cimma yarjejeniya kan batun yankuna. Rahoton dai na zuwa ne daga kamfanin dillancin labarai na AFP.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!