Connect with us

Labarai

Rashawa : Magu ya kalubalanci rahoton kwamitin Ayo Salami

Published

on

Lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu ya kalubalanci rahoton da kwamitin Ayo Salami ya fitar da ke baiwa shugaban kasa shawarar cire shi don yanke masa hukunci kan tuhume-tuhume da ake yi masa.

Lauyan Ibrahim Magu Wahab Shitu ya ce ya zuwa yanzu bai gama tattara bayanan da zai gabatar da su ba, duk kuwa da sauraron korafe-korafe da kwamitin Salami ke yi.

Ya kara da cewa bayan zarge-zarge da ake yi wa dakataccen shugaban hukumar yaki a rashawan, kwamitin basu fito da kofin tuhume-tuhumen da suke yi akan sa ba.

Shittu har ila yau ya kara da cewa, matsayin sa na lauyan Ibrahim Magu bai samu damar ganin takardun tuhume-tuhumen ba da sauran zarge-zargen da ake yi wa Magu ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!