Labarai
Rashin aikin yi ya karu da kaso 27% a bana – NBS
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce, adadin wadanda basu da aikin yi a kasar nan ya karu daga kaso 23 zuwa sama da kaso 27 na tsakiyar shekarar da muke ciki wanda adadin ya zarta na shekarar 2018.
Hakan ne cikin wata kididdigar da hukumar ta fitar a baya baya nan, na adadin wadanda basu da aikin yi a kasar nan.
NBS ta ce adadin ya karu daga kaso 20 na kaso dayan shekarar 2018 zuwa sama da kaso 28 a kaso biyun shekarar da muke ciki.
Kididdigar ta NBS na nuna cewa, a kaso biyun farko na wannan shekara rashin aikin yi a kasar nan tsakanin matasa dake tsakanin shekara 15 da 34 ya karu daga kaso 29 zuwa sama da kaso 34, yayin da wadanda suke tsakanin wadannan shekaru kuma suke da ayyukan yi ya karu daga kaso 25 zuwa sama da kaso 28 kwatankwacin kaso ukun shekarar 2018.
Hukumar ta NBS ta kara da cewa, wannan adadi shi ne mafi yawa da aka taba gani, idan aka kwatanta da sauran shekaru a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login