Labarai
Rashin bayyanar El-rufa’i da lauyansa ya janyo tsaiko a tuhumar sa da rashawa da cin hanci

Rashin bayyanar tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i da babban lauyan sa a zauren babbar kotun jihar Kaduna ya haifar da tsaiko ga fara sauraron shaidu akan tuhumar rashawa da cin hanci da hukumar ICPC ke yi masa.
Tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne kotun ta sanya yau litinin da gobe talata a matsayin ranakun da hukumar ta ICPC zata fara gabatar da shaidun ta akan zargin almundahanar kudaden gwamnati yayin da El-Rufai ke gwamnan a jihar Kaduna.
A yayin zaman kotun na yau Litinin, mai shari’a Darius Khobo ya umarci hukumar ta ICPC ta gabatar da tsohon gwamna Malam Nasiru El-Rufai a zauren kotun gobe talata domin fara gabatar da shaidun ta.
Alkalin kotun mai shari’a Darius Khobo ya dage zaman sauraron karar zuwa gobe talata, idan Allah ya kai mu.
You must be logged in to post a comment Login