Connect with us

Labarai

Sojoji sun hallaka yan tada kayar baya na ISWAP fiye da 40

Published

on

Rundunar Soji ta Operation Hadin Kai ta ce, ta hallaka mayakan kungiyar ISWAP sama da arba’in a wani harin sama da ta kai musu a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana cewa an kai harin ne a ranar goma ga watan Oktoba a kauyen Badu, kudancin Gudumbali, da ke karamar hukumar Guzamala.

 

Ya ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa mayakan na shirin kai hare-hare kan sojojin da ke aiki a yankin Sector Three. Rundunar ta fara sa ido kan motsin mayakan kafin ta kai harin kan wani gini da suke ciki.

 

Haka kuma, ya kara da cewa, bayanan farko sun nuna cewa harin ya hallaka mayakan sama da arba’in, ciki har da wani babban kwamandan ISWAP.

 

Kyaftin Mohammed Goni ya kuma ce, an lalata motoci biyu da babura kusan ashirin da mayakan ke amfani da su wajen zirga-zirga da kai hare-hare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!