Kiwon Lafiya
rashin bibiya da tsari shi ke kara yawan Masu zaman banza
Cibiyar horas da Matasa sana’o’in dogaro da kai ta Abacha Youth Centre da ke nan Kano, ta bayyana rashin bibiya da yin tsari kan Matasan da aka koya wa sana’o’in dogaro da kai a matsayin hanyoyin da ke kara yawan Matasa marasa aikin yi a fadin kasar nan.
Daraktan sashen hulda da jama’a na cibiyar Kwamared Yahaya Shuaibu Ungogo ne ya bayyana hakan a jiya ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan Freedom Rediyo.
Ya ce, rashin bin diddigin matasan da aka horas hakan kan sanyasu sayar da kayan tare da cinye kudin cikin kankanin lokaci.
Ya kara da cewa rashin sanya idon gwamnati akan wasu daga cikin kayayyakinta na koyar da matasa sana’o’i na kara haifar da matsaloli da dama a kan kayan koyar da sana’o’in.
Haka zalika ya kuma ce, kamata ya yi kafin gwamnati da masu hali su tura matasa don koyon sana’o’in to akwai bukatar nazartar irin wadanda za’a rika tura wa don gudun tura wadanda za su yi wasa da damar.
Kwamared Yahaya Shuaibu Ungogo, ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su baiwa tsarin koyar da matasa sana’o’i muhimmanci ta hanyar ware kudade masu dama duba ga irin alfanun da hakan ke da shi.