Labarai
Rashin dorawa akan ayyukan gwamnati na haifarwa Najeriya matsaloli – Masani
Masanin tattalin arziki na kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi Dr. Abdussalam Kani yace rashin cigaba da dora ayyukan da gwamnatocin baya ke yi na daga cikin manyan matsalolin da shugabannin kasar nan ke haifarwa al’ummar Najeriya.
Malam Abdussalam Kani ya bayyana haka ne ta cikin shirin duniyar mu a yau na tashar Freedom Radio.
Abdussalam Kani ya kara cewa idan akayi duba kan tsofaffin shugabannin Najeriya da suka gabata akwai wadanda sukayi watsi da wasu manyan ayyukan da yakamata ace sabbun Gwamnatoci sun dora amma sukayi watsi da ayyukan wanda a yanzu matsalolin ke bayyana.
Malam Kani ya kara da cewa hatta bashin da gwamnatin Najeriya ke shirin ciyowa a yanzu na daga cikin sharuddan bada bashin ciki harda kara kudin wutar lantarki da kuma kara farashin man fetur wanda a yanzu al’ummar kasar ke cigaba da kokawa dashi.
Anasa bangaren Kwared Safiyanu Bichi daya kasance cikin shirin cewa yayi rufa rufa da babban bankin bada lamuni na duniya IMF suke kakabawa shuwagabannin wannan kasa idan zasu karbi bashi wata illace babba.
Ya kara da cewa matsalar rashin gina al’ummar wannan kasa da shugabannin keyi musamman samarwa da ‘yan kasa ayyukanyi da abinci na daga cikin matsalolin wannan kasa.
Yana mai cawa batun cinhanci da rashawa daya dabai baye kasar nan na daga cikin abunda ke cigaba da haifarwa da Najeriya koma baya, baya ga watsi da wasu ayyukan raya kasa da wasu gwamnatoci keyi a yanzu.
Malam Riya’udden Zubairu Maitama wanda shima ya kasance cikin farin cewa yayi tun daga lokacin da Najeriya ta samu ‘yancin kai zuwa yanzu ana fitarda sabbin tsaruka na ciyarda kasa gaba amma rashin aiwatardasu shine babban abunda ke yiwa tsarukan kasar tarnaki saboda sakaci irin nasu.
Riya’uddeen ya kara da cewa duk irin sabbin tsare – tsaren da ake kawowa kasar nan babu wani guda daya da yake aiki sai dai a rika baro sabbin ayyuka wanda kuma haka wata babbar illace ga al’ummar kasa.
Ya kara da cewa tattalin arziki Najeriya ya fada cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin wasu ayyuka da suka hada da matsalar tsaro , rashin samarda ingantaccen Ilimi baya ga matsalar karancin wutar lantarki da sauran abubuwa more rayuwa.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya bibiyi yadda shirin ya gudana ya ruwaito cewa dukkanin bakin da suka kasance cikin shirin na cewa matukar ba’a sauya tsarin tafiyar da Najeriya ba shakka babu kasar zata cigaba da fuskantar matsalar tattalin arki.
You must be logged in to post a comment Login