Labaran Kano
Rashin ilimi na kawo koma baya a fannin rayuwar matasa- Dagacin Gwazaye
Dagacin Gwazaye dake Karamar hukumar kumbotso a nan kano Malam Umar Ali, Ya ce rashin tura yara makaranta da bibiyar karatunsu shi ke kawo koma baya a fannin rayuwa.
Dagacin ya bayana hakan ne lokacin bikin saukar alkur’ani karo an farko na dalibai 12 wanda ya gudana a makarantar Talle Islamiyya Littahafizul Kur’an dake Unguwar Gangar Ruwa a yankin na Gwazaye.
Mal Umaru Ali,Ya kara da cewa rayuwar yaran da aka tura makaranta tana inganta harma su zamo abun alfahari ga iyayensu dama sauran Al’umma yayin da wadanda basu samu ilimi ba rayuwarsu ke taggayara.
Da yake nasa jawabin mataimakin kwamandan hukumar Hisba ta jihar kano sashin ayuka na musamman Malam Muhammad Albakari, cewa yayi ba dai dai babe suna con mutuncin malamai musamman a gaban dalibai wanda hakan ke kore Albarkar Ilimin.
A nasa jawabin Daraktan makarantar Malam Abubakar Umar Assayyadi, bukatar Iyaye yayi da su cigaba da basu hadin Kai wajen bayar da Ilimi gami da tarbiyya.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad,Ya ruwaito cewar Daliban da suka sauke Al’kur’ani mai girman sun hadar da mata biyar da maza Bakwai.