Labarai
Rashin kayan aiki ke kawo koma baya a yaki da cin hanchi da rashawa – ICPC
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ICPC ta bayyana damuwar ta kan rashin samar da ofisoshin shiyya-shiyya da kuma rashin kudaden gudanar da ayyuka hukumar.
Shugaban hukumar reshen Jihar Kano da Jigawa Alhaji Ibrahim Garba Kagara ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kamala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom radio.
Muhammad Kagara ya ce, ba wai iya kamfanoni hukumarsu take bibiya ba har da ma’aikatun gwamnati da ma ita kanta gwamnatin, matukar tayiwa al’umma alkawari kuma ta gaza cikawa.
“Babbar matsalar mu ita ce yadda hukumarmu bata da ofisoshi a kananan hukumomi, kuma bau da isassun kudin da za mu rika aiwatar da wasu muhimman ayyukan wanda sune manyan kalubalen da ke hana ayyukan mu ci gaba”
Sai dai shugaban ya bukaci mahukunta da su tallafawa hukumar don samar da kayan aikin da za su kawo karshen ayyaukan masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
You must be logged in to post a comment Login