Labarai
Rashin kudi da man fetur zai haifar da tasgaro ga zaben kasar nan: Kamilu Sani Fagge
- Rashin samun sabbin takardun Naira ka iya shafar gudanar da babban zaben kasa da ya rage kwanaki 10 kacal.
- Hukumar zabe na bukatar kudi domin ta samu damar daidaita harkokin tsaro da kayan aiki, kuma karancin naira na iya shafar hakan.”
- shakka babu rashin kudin zai kawowa zaben tasgaro, ta hanyar hana mutane su fita su kada kuri’ar.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ce rashin samun sabbin takardun Naira ka iya shafar gudanar da babban zaben kasa da ya rage kwanaki 10 kacal.
Kwamishinan zabe Alhaji Yahaya Bello ne ya bayyana hakan, a Abuja, har ma ya ce, “hukumar na bukatar kudi domin ta samu damar daidaita harkokin tsaro da kayan aiki, kuma karancin naira na iya shafar hakan.”
Kan hakan ne Freedom Radio ta zanta da masanin siyasar a jami’ar Bayero da ke Jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge don jin yadda rashin kudin zai iya tasiri a babban zaben kasa.
wanda ya ce ko baya hukumar ta bayyana cewa bata da kudi, sai dai kuma ta fito daga baya tace babban bankin ya bata isashshen kudin da zai isheta ta udanar da zabe, sai kuma gashi yanzu ta kara fitowa ta kara kokawa kan rashin kudin, masanin ya ce wannan ka iya sanya shakku a zukatan mutane, wanda ka iya haifarwa zaben matsala, da kuma kara sanyawa jikin mutane yayi sanyi, har su kasa fitowa kada kuri’a.
A don haka Habu fagge yace wajibi ne a fito a shawo kan wannan matsalar ta rashin mai, data rashin kudi, shakka babu zai kawowa zaben tasgaro, tahanyar hana mutane su fita su kada kuri’ar.
Rahoton:Rahma Muhammad
You must be logged in to post a comment Login