Labarai
Rashin kudi ne ya hana mu daga darajar ma’aikata- Hukumar bayar da ruwa ta Kano

Hukumar bayar da ruwan sha ta jihar Kano, ta ce rashin kuɗi a hukumar ne ya sanya ta gaza mayar da ma’aikatan wucin gadi zuwa matsayin na din-din-din.
Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana hakan bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin ruwa na majalisar dokokin Kano.
Injiniya Garba Ahmad Bichi, ya ce, a cikin kasafin da aka ware wa hukumar za su gyara tare da samar da sabbin matatun ruwa.
You must be logged in to post a comment Login