Siyasa
Rashin lafiya ta hana Sanata Dino Melaye halartar zaman kotu
Sanata mai wakiltar yammacin Kogi Dino Melaye bai halacci zaman kotu ba a yau.
Sanata Dino Melaye dai yana fuskantar tuhuma ne sakamakon mallakar bindigu ba bisa kaida ba amma duk da haka lauyoyin dino Melaye sunce bashi da lafiya.
Amma wasu mutane biyu da ake zargi tare da Dino Melaye Kabir Saidu wanda aka fi sani da Osama da Nuhu Salihu wanda ake kira da suna Smally sun halacci zaman kotun na yau domin amsa tuhume tuhumen da ake yi musu.
Lauyoyi masu kare Dino Melaye Barrister Yemi Muhammad wanda ya wakilci Chief Mike Ozekome yace Sanata Dino Melaye bai halacci zaman kotun ba saboda bashi da lafiya.