Labarai
Rashin sanin dabaru ke sa daliban aikin Noma rasa abinyi – CDA
Cibiyar dake bincike kan harkokin Noma a kasashe masu Zafi a jami’ar Bayero wato Center For Dry Land Agriculture ta ce duk mutumin da ya samu horo na musamman a fannin Noma ba zai taba rasa aikin yi ba.
Shugaban cibiyar Farfesa Jibrin Mohammed Jibrin ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin horon da cibiyar taiwa dalibai 50 da suka karanci aikin Noma domin su Dogara da kansu a fannin.
Farfesa Jibrin ya kuma ce sun shirya taron ne dan magance, rashin aikin yi ga daliban da suka karanci fannin na Noma.
Daliban da suka lakanci dabarun dai sun kasan ce wadan da suka kammala jami’ar da kuma wadan da ke karatu a ciki.
Taron ya gudana a cibiyar binciken aikin Noman dake jami’ar ta Bayero, a ranar Litinin 06/01/2025.
You must be logged in to post a comment Login