KannyWood
Rashin sanya jarumai a guraban da suka dace zai durkusar da Kannywood – Abdul M. Sheriff
Jarumi kuma mai shirya fina-finai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Abdul’azeez Muhammad Shareef wanda akafi sani da Abdul M. Shareef ya ce rashin saka jaruman da suka da ce a wasu fina-finai na daya daga cikin matsalolin dake durkusar da masana’antar.
Shareef ya bayyana hakan ne a cikin shirin Zauren Kannywood na gidan Rediyo Freedom Kaduna a yau Lahadi.
Ya ce, akwai labarai masu muhimmanci dake dauke da sakon da al’umma zasu amfana, amma rashin sanya jauruman da suka da ce da hawa labarin shi ke haifar da koma baya, lamarin daya alakantashi da bukatar kashin kai ta wasu masu shirya fina-finai.
Duba da yadda masana’antar keda fadi, Abdul M Shareef ya ce akwai kalubale babba ga shugabanninsu kan su tsaya kai da fata domin tafi da ita yadda ya kamata, ba tare da nuna bam-bamci ba.
A karshe ya bai wa masoyansu hakuri kan korafe-korafen da a wasu lokutan ake samu na rashin basu lokaci, koda yake yace wasu lokutan wasu na zuwa ne da fuska biyu, sada zumunta ko kuma akasin haka.
You must be logged in to post a comment Login