Labarai
Rashin shan ruwa isashe barazana ce babba ga lafiyar ‘dan adam: Abubakar Muhammad Isah
- Yawan shan ruwa mai yawa zafi na Da mahimmanci ga lafiyar dan adam/
- Rashin shan ruwan na haifar da matsaloli ga lafiyar ‘dan adam
- Matsalolin sun hadar da bushewar fatar jiki da dai sauransu
Wani jami’in lafiya a asibitin kashi na Dala a Jihar Kano Abubakar Muhammad Isah ya ce ‘yawan shan ruwa mai yawa musamman a wannan lokaci na zafi yana da matukar mahimmanci a jikin ‘dan adam’.
Abubakar Muhammad Isah ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan muhimmancin shan ruwa a lokacin zafi.
Ya kuma ce, ‘rashin shan ruwa na haifar da bushewar fata da daskarewar jinni da dai sauransu’.
‘Haka zalika rashin ruwa a jikin ‘dan adam kan jawo masa matsaloli da dama ciki harda bushewar fatar jiki da dai sauransu.
Abubakar Muhammad Isah ya kuma ce ‘a lokuta da dama idan mutum yana jin ba dadi a jikinsa, yasha ruwa sosai zai ji ya samu lafiya.
Rahoton:Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login