ilimi
Rashin tsaro: Mun rasa malamai sama da ɗari 8 a Arewa maso Gabas
Ƙungiyar malaman makarantu ta ƙasa NUT ta ce, sama da malamai ɗari takwas ne suka rasa rayukan su sanadiyyar ayyukan ta’addanci a sassan ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa Dakta Nasir Idris ne ya bayyana hakan, a zantawar sa da manema labarai a ƙarshen mako.
Shugaban yayi barazanar cewa, za su janye malamai da ɗalibai a makarantun da ba su da isasshen tsaro a faɗin ƙasar nan.
Dakta Nasir Idris, ya kuma ce akwai malamai da ɗalibai da dama da aka sace a sassan ƙasar nan, musamman ma a arewa maso gabashin kasa nan a shekarar 2021.
Ya kara da cewa fara aiwatar da sabon tsarin biyan albashi zai taimaka matuka wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login