Kiwon Lafiya
Rashin wadatattun likitoci ya sa kowanne likita ke ganin mara lafiya¬ 1800 a rana – NMA
Kungiyar likitoci ta ƙasa NMA reshen jihar Kano ta koka kan rashin wadatattun likitoci a kasar nan.
Shugaban ƙungiyar ana Kano Dakta Usman Aliyu ne ya bayyana hakan.
Ya ce “Rashin wadatattun likitoci a ƙasar nan ya sa kowanne likita ke ganin mutane 1800 a kowacce rana, domin kuwa a yanzu Kano na da likitoci sama da dubu 1, 600 waɗanda su ke duba marasa lafiya a asibitocin jihar.
Sai dai ya tabbatar da cewa akwai matsalar likitocin a faɗin ƙasar nan, wanda hakan ke da nasaba da irin matsalolin da mutane ke fuskanta.
“Adadin al’ummar jihar Kano a yanzu ya kai sama da miliyan 20, wanda hakan ta sa likitocin ke iya ganin mutane 1800 a duk rana” inji Dakta Usman Aliyu.
Wannan dai ya biyo bayan yadda har yanzu likitoci masu neman ƙwarewa suka gaza janye yajin aikin da suka shafe kwana 60 suna yi.
You must be logged in to post a comment Login