Connect with us

Labarai

Rashin wutar Lantarki na taka rawa wajen karuwar fadan daba- Yan K/Naisa

Published

on

Mazauna  unguwanni Kofar Na’isa da Lokon Makera a Kano, sun koka da cewa rashin wadatacciyar wutar Lantarki ya jefa su cikin damuwa sakamakon yadda ɓata gari ke tayar da rikicin daba musamman ma a yan kwanakin nan.

Haka kuma mazauna yankunan, sun bayyana damuwa kan yadda suka kasance cikin halin duhu na tsawon lokaci bayan lalacewar Taransifomar su.

Mutanen sun kuma bayyana cewa duk inda ya kamata su nemi tallafi kama daga wajen mahukunta da sauransu sun bi amma abun ya ci tura.

A zantawarsu da Freedom Radio wasu daga cikin matan yankunan, sun roki gwamantin Kano da shugaban ƙaramar hukumar Gwale da su kai musu ɗauki.

Malam Dauda Lokon Makera na daga cikin Dattijan unguwar ya ce, kamata ya yi ƴan majalisa su mayar da hankali kan ayyukan da ya kamata ba wai rigima kan an bayyana wanda ya fi aiki a cikin su ba.

Sai dai duk ƙoƙarin da Freedom Radio ta yi na jin ta bakin ƙaramar hukumar ta Gwale da yankunan ke karkashinta, abun ya ci tura, sai dai za mu ci gaba da bibiyar wannan matsala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!