Labarai
Raunin akida ne ke haddasa yawaitar sauya sheƙa- Ganduje

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce raunin akidar siyasa a jam’iyyun Najeriya ne ke haddasa yawaitar sauya sheƙar ‘yan siyasa daga wannan jam’iyya zuwa waccan.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yin tsokaci kan yawaitar sauya sheƙar wasu manyan ‘yan siyasa zuwa APC, inda ya ce, mafi yawan jam’iyyun siyasar ƙasar ba su da bambancin manufofi da akidu da za su riƙe mambobinsu.
Ya ƙara da cewa a tsarin dimokuraɗiyya, kowane ɗan ƙasa yana da ‘yancin shiga jam’iyyar da yake so, yana mai jaddada cewa yawaitar masu komawa APC na nuna yadda jam’iyyar ke ƙara samun karɓuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login