Labarai
Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan Titin Lagos-Calabar zuwa sunan zhugaba Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan Titin Lagos-Calabar Coastal Highway zuwa President Bola Ahmed Tinubu Coastal Highway. Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce an dauki matakin ne domin girmama rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka wajen kirkiro da wannan shiri tun yana gwamnan jihar Legas.
Umahi ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya kuma ce Shugaba Tinubu ya amince da karin kilomita 400 a aikin Fourth Legacy Highway, wanda hakan zai kara tsawon titin daga kilomita 700 zuwa kilomita 1,100, tare da fadada shi zuwa jihar Taraba.
Ministan ya kuma ce shugaban kasa ya amince da sake gina wasu sassan Titin Lagos-Ibadan da fadada wani bangare na Titin East-West, tare da kammala aikin gadar Ibi a jihar Taraba da kuma gina gadar Lao mai tsawon kilomita 5.76.
A cewarsa, wadannan ayyuka na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na inganta hanyoyin sufuri, bunkasa tattalin arziki da kuma inganta muhimman ababen more rayuwa a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login