Labarai
Shugaba Tinubu zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 UNGA da za a buɗe a birnin New York na ƙasar Amurka a watan Satumba.
Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Tinubu a ranar Laraba.
Jimoh Ibrahim ya ce Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa zai halarci taron, inda ake sa ran zai gabatar da jawabi ga shugabannin ƙasashe da wakilan duniya kan muhimman batutuwan da suka shafi Najeriya da kuma harkokin duniya.
Ana sa ran halartar Shugaba Tinubu a taron zai ba Najeriya damar ƙara bayyana matsayinta kan batutuwan siyasa, tattalin arziki, tsaro da ci gaba mai ɗorewa a matakin ƙasa da ƙasa.
Za a gudanar da taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a hedikwatar Majalisar da ke New York a watan Satumbar shekarar nan.
You must be logged in to post a comment Login