Labaran Wasanni
Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar La Liga ta kasar Andalus a karo na 35 bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Espanyol da ci 4-0 a ranar Asabar, a filin wasa na Santiago Barnabaue.
Real Madrid dai ta lashe gasar karkashin jagorancin Carlo Ancelotti, wanda ya maye gurbin Zinedine Zidane a tawagar ta Los Blancos.
Tunda fari dai dan wasa Rodrygo ne ya fara zura kwallon farko a minti na 33 da na 43 dab da za aje hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Real ta kara kwallo ta uku a minti na 55 ta hannun dan wasa Marco Asensio, yayinda a minti na 81 jagoran ‘yan wasan kungiyar Karim Benzema ya tabbatar da nasarar ta Madrid a wasan.
Kawo yanzu dai Real Madrid ta fi ko wacce kungiya lashe gasar, inda jumulla ta lashe har sau 35 a tarihi, sai Barcelona da ke da 26.
To sai dai Real Madrid bayan lashe gasar La Liga da ta yi zata fuskanci tawagar Manchester City a gasar cin kofin zakarun turai zagaye na biyu a mako mai zuwa a filin wasa na Santiago Bernabéu
Bayan da suka tashi wasan farko da ci 4 da 3 a filin wasa na Etihad da ke Ingila a makon da ya gabata.
An fara gasar La Liga a shekarar 1929 wanda kawo yanzu shekaru 93 kenan, inda Barcelona ta ka sance kungiya ta farko da ta fara lashe gasar a tarihi.
You must be logged in to post a comment Login