Labarai
Rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa ya yi sanadiyyar hallaka mutum 100 a Guinea
Ana fargabar kimanin mutane 100 sun rasa rayukansu a wani rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar kasar Guinea a yammacin jiya Lahadi.
Rikicin dai ya barke ne a lokacin da ake tsaka da buga wasan wanda aka shirya don karrama shugaban mulkin sojin kasar Janar Mamadi Doumbouya.
Wasu jami’an lafiya da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, Asibitin birni na biyu mafi girma a kasar ya cika makil da gawarwaki.
Wasu faya-fayan bidiyo da aka rika yadawa a kafafan sada zumunta sun nuna yadda fusatattun masu kallon wasu suka rinka gwabza fada da juna, har suka fantsama kan tituna.
You must be logged in to post a comment Login