Connect with us

Labarai

Rikicin cikin gida a jam’iyyun adawa alama ce ta rashin shirin su na lashe zaben 2027

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa alama ce ta rashin shirin su na iya karbar shugabancin ƙasar nan a zaben 2027.

 

Nentawe ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce duk wata jam’iyya da ba za ta iya gyara matsalolinta na cikin gida ba, ko haɗa kai tsakanin mambobinta, ba za a iya amincewa da ita ta jagoranci ƙasa mai miliyoyin jama’a.

 

Yilwatda ya ƙara da cewa rikice-rikice da rabuwar kai da kuma shari’o’i da rashin tsari da ake gani a jam’iyyun adawa, duk suna nuna gazawa da rashin ƙwarewa wajen tafiyar da al’amura.

 

Ya kuma buƙaci ‘yan kasar nan su rika bambance tsakanin hayaniya da ƙwarewa da kuma farfaganda da shiri na gaskiya, da kuma son zuciya da nagartaccen shugabanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!