Labarai
Rikicin NNPP mu gaba ta kaimu – APC
Jam’iyyar APC ta ce, rikicin da ya kunno kai a jam’iyyar NNPP gaba ta kai su.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Aruwa ya ce, samun rabuwar kai da aka yi tsakanin Kwankwaso da Shekarau gaba ta kai su gobarar titi a Jos.
“Tsakanin Kwankwaso da Shekarau babu wata hanya da za su hadu domin gudanar hulda irin ta siyasa, domin kowa yana ganin ya kai geji a rayuwa ta yadda babu wanda zai yiwa wani wayo”. Inji Aruwa.
“Mu wannan sabanin da jagororin biyu suka samu nasara ce a gare mu, kuma dukkan su suna yi ne a kan abinda ya shafe su da kuma irin bukatun su da suke da shi da kuma ra’ayin su”.
Ahmad S. Aruwa ya kuma ce, dukkan kalmomin da shuwagabannin ke fada kan yunkurin hade kasar nan guri guda tare da samar da sabuwar gwamnati abun ya zama ba daidai ba.
A yau Litinin 22 ga watan Agustan shekarar 2022 ake sa ran ficewar Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bisa zargin yaudararsa da jam’iyyar NNPP ta yi wajen fitar da yan takara, duk da yunkurin da yayi na bibiyar jagoran jam’iyyar Rabi’u Musa Kwankwaso.
Haka kuma yayi zargin cewa, jam’iyyar ta fitar da kujerun wadanda za su tsaya takara na majalisar tarayya da na dattijai ba tare da an baiwa mutanen sa ba.
You must be logged in to post a comment Login