Labarai
Romon Dimukraɗiyya: Hadimin Ganduje ya raba wa matasa Jakuna

Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran matasa Murtala Gwarmai ya yi rabon jakuna ga matasa.
Murtala Gwarmai mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran matasa, tare da kwamishinan matasa na Kano Kabiru Ado Lakwaya a yayin bikin rabon tallafin.
Gwarmai ya raba jakunan ne a cikin jerin tallafin da ya raba wa matasa.
A cewar sa, akwai matasa da dama da aikin su shi ne sayar da ƙasa ta hanyar amfani da jakuna.
Kuma sun faɗa masa ba abin da suke buƙata kamar a basu jakuna domin bunƙasa sana’ar su.
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano Kabiru Ado Lakwaya, a wajen bikin rabon tallafin.
Murtala Gwarmai ya kuma raba wa matasan baburan hawa da keken hawa, da kuma kuɗi ga matasan.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
Wasu cikin kayayyakin da aka rarraba.
You must be logged in to post a comment Login