Labarai
Dortmund ta kawo karshen wasanni 24 da Barcelona ta kara

Kungiyar kwallon kafa ta Dortmund, ta kawo karshen wasanni 24 da Barcelona ta kara ba tare da rashin nasara ba
Borussia Dortmund ta samu nasara kan Barcelona, da hakan ya kawo karshen wasanni 24 da suka buga ba tare da doke su ba.
A karawar da kungiyoyin suka yi a ranar Talata a gasar zakarun nahiyar turai, inda kungiyar ta kasar Jamus ta doke Barcelona da ci 3-1.
Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara tun cikin Disamba, bayan da Atletico Madrid ta doke ta da ci 2-1.
You must be logged in to post a comment Login