Labaran Kano
Rotary ta bawa hukumar KAROTA tallafin kayan bada hannu
Daga Shamsu Dau Abdullahi
Kungiyar Rotary Club ta kaiwa hukumar Karota ziyara domin nuna mahimmanci da hukumar take bayarwa na tsaftace ka’idojin hanya.
Shugaban kungiyar Rotary Bidemi Nuradden yace sun kawo tallafin ne domin nunawa sauran kungiyoyi su rika tallafawa hukumomin tsaro da kayan aiki na bada hannu.
Ya kara da cewa wannan abun yana da mahimmanci a wajen bada hannu a kan titi musamman ma titunan da ‘’yan makaranta suke tsallakawa zuwa gida da makaranta.
Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA
Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna
Shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Dan Agundi yace suna son kungiyoyi su rika taimakawa hukumomin tsaro domin ta hakane za’a samu cigaba a jihar Kano.
Nan take hukumar ta Karota ta fara raba kayan da kungiyar ta kawo hukumar.