Labarai
Rufe kan iyaka yasa muna sayar da shinkafa Tirela dari a rana
Hukumar hana fasakwauri ta kasa tace rufe kan iyakar Najeriya yayi sanadin cafke bakin haure 146 da suka shigo kasar nan ba bisa kaida ba a kwanaki arbain da suka gabata.
Jamiin hulda da jamaa na hukumar ta hana fasakwauri na kasa kuma mataimakin babban kwantrola Joseph Attah ne ya bayyana haka a cikin shirin Barka da Hantsi da ya tattauna akan wayar da kan masu ruwa da tsaki na dalililan rufe kan iyakokin Najeriya.
Joseph Attah yace ba wai kawai hana shigo da shinkafa ce alfanun rufe kan iyakar Najeriyar ba, hatta masu shigo da makamai kasar nan an yi musu tarnaki.
Yace wasu bangarori da rufe kan iyakar ya haifar ya hada da kwace buhuhuna na taki wanda ake hada ababan fashewa da su.
A nasa bangaren shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu da aikin gona KACCIMA ta Jihar Kano Alhaji Dalhatu Abubakar yace sakamakon rufe kan iyakar masu kamfanin shinkafa ire-iren su, suna iya sayar da Tirelar shinkafa da ta kai 100 a rana.
Da yake tsokaci Alhaji Auwalu Mariri na kasuwar Singa yace rufe kan iyakar ya saka su tilas su rika sayan shinkafar da aka sarrafa ta a gida Najeriya.