Labarai
Runduna Yan Sanda ta kara yawan jami’ai a iyakokin Kano da Katsina

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa, ta dauki matakin kara yawan jami’an tsaro a kan iyakokin jihar Kanon da makwabciyarta Katsina mai fama da matsalar tsaro.
Jam’in hulda da jama’a na hukumar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Litinin.
Haka kuma rundunar, ta bukaci mazauna yankunan da ke kan iyakokin da su taimaka wa jami’an tasaro da bayanan sirri kan duk wani motsi da ba su aminta da shi ba.
You must be logged in to post a comment Login