Labarai
Rundunar ƴan sanda ta ja kunnen waɗanda ba su da alaƙa da shari’a gwamnan Kano waje zuwa kotu
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta gargaɗi mutanen da ba su da alaƙa da shari’ar zaɓen Gwamnan Kano da kotun karɓar ƙorafin zaɓen Gwamna za ta yanke da su kaucewa zuwa kotun.
Mai magana da yawun rundunar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce, Rundunar da sauran jami’an tsaro za su tabbatar da cewa an ci gaba da samun zaman lafiya kafin da lokacin shari’ar har ma bayan yanke hukuncin shari’ar karar da jama’iyar APC ta kai Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, da Jama’iyar NNPP da kuma hukumar zabe INEC game da sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a farkon shekarar nan da muke ciki.
Kiyawa ya kuma ƙara da cewa rundunar ba za ta lamunci kowane irin yunƙurin tayar da tarzoma ba ko kawo barazana ga harkokin tsaro.
You must be logged in to post a comment Login