Labarai
Rundunar Civil Defence ta bukaci hadin kan mutanen Kano

Hukumar tsaro ta Civil Defence shiyyar Kano, ta bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da ba da gudummawa wajan tallafawa harkokin tsaro.
Shugaban hukumar Muhammad Hassan Agalama ne ya bayyana hakan lokacin bikin ranar Civil Defence ta Duniya na bana.
Da yake jawabi a madadin shugaban hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce dole sai an samu haɗin kai tsakanin al’ummar gari da kuma hukumar ta su, kafin a cimma daƙile harkokin rashin tsaro a faɗin jihar.
You must be logged in to post a comment Login