Connect with us

Labarai

Rundunar Civil Defence ta kama mutane 6 da ake zargi da lalata bututu mai

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defence ta kama mutane 6 da ake zargi da lalata bututu tare da satar man fetur a yankin Pagada da ke a Karamar Hukumar Gwagwalada ta Birnin Tarayyar Abuja.

Wannan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar, DSC Monica Ojobi, ta fitar.

Ta ce jami’an rundunar sun kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 3:30 na dare a ranar Asabar 18 ga Yuli, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da ake zargin suna yi a kusa da bututun.

Sanarwar ta ce, an kama su ne yayin da suke dibar man fetur suna durawa jarkoki bayan sun huda bututun da injin huda karfe.

Rundunar ta kwato babura biyu, jarkoki hudu masu dauke da man fetur, shebur daya, bindigogi gida biyu da injin huda karfe daya da ake zargin an yi amfani da shi wajen lalata bututun.

NSCDC ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!