Labarai
Jami’an NSCDC sun kama dalibai sakamakon bikin kammala Sakandire

Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Adamawa ta kama dalibai 10 da ake zargin sun karya dokar hana bikin kammala sakandare da aka fi sani da “Signed Out.”
Kakakin hukumar a jihar, DSC Nyako Amidu Baba, ya ce jami’an Safe School Response Squad sun gudanar da kamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu daliban makarantun Capital School, GDSS Demsawo, Doubelli da Damilu.
A cewarsa, an zargi matasan da yin fentin jiki, yaga kayan makaranta, fada a kan tituna da kuma wasu ayyukan da ka iya tayar da hankalin jama’a.
Hukumar ta ce gwamnatin jihar Adamawa ta haramta bikin “Signed Out” tun a shekarar 2025, bayan yawaitar korafe-korafe kan tashin hankali da rashin da’a da ake alakanta da shi.
NSCDC ta kuma bayyana cewa binciken farko ya nuna wasu daga cikin mahalartan sun sanya kaya masu tayar da zargi, tare da zargin kwace wayoyin hannu da sauran kayayyakin jama’a.
Haka kuma, an gano cewa daya daga cikin wadanda aka kama ba dalibi ba ne duk da yana sanye da kayan makaranta, yayin da wasu kuma daliban SS1 da SS2 ne, ba masu kammala karatu ba.
Kwamandan NSCDC na jihar Adamawa, CC Nasiru Saleh, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano duk wadanda ke da hannu a lamarin, tare da karfafa hadin gwiwa da hukumomin makarantu domin hana sake faruwar irin wannan abu.
You must be logged in to post a comment Login