Labarai
Gwamnatin Kano ta ware 25 da 31 ga Yuli domin aikin tsaftar Muhalli

Gwamnatin Jihar Kano ta Ware 25 da Kuma 31 Ga Yuli da muke ciki Domin Aikin Tsaftar Muhalli a fadin jihar.
An cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin da aka gudanar a yau a dakin taro na Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano.
Da yake jawabin shugaban kwamitin Barista Mustapha Nuradden Muhammad ya ce an kira taron ne domin duba yadda aka gudanar da ayyukan tsaftar da suka gabata, tantance kalubalen da aka fuskanta da kuma tsara hanyoyin inganta shirin a nan gaba.
Bayan doguwar tattaunawa, kwamitin ya yanke shawarar ware ranar Juma’a, 31 ga Yuli, domin gudanar da tsaftar muhalli a ofisoshin gwamnati, kasuwanni, tashoshin mota, masana’antu da wuraren kasuwanci a fadin jihar.
Haka kuma, an ware ranar Asabar, 25 ga Yuli, domin tsaftar gidaje da unguwanni, kamar yadda aka saba inda ake sa ran mazauna jihar za su tsaftace muhallansu tare da zubar da shara a wuraren da gwamnati ta amince da su.
You must be logged in to post a comment Login