Kiwon Lafiya
Rundunar sojan kasar nan ta sanar da hallaka yan bindiga dadin 35
Rundunar tsaron kasar nan ta sanar da hallaka ‘yan-bindiga 35 sannan jami’in Soja daya ya mutu yayin da guda ya bata, lokacin bata-kashi a Jihohin Benue da Nassarawa da Taraba da kuma Zamfara.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labaran shelkwatar Birgediya Janar John Agim ya bayar jiya yana mai cewa sun gudanar da wani samame ne a karshen makon da ya gabata a wadancan Jihohi 4.
John Agim ya bayyana cewa sun durfafi kauyukan Umaisha da Kolo a kananan hukumomin Toto da kuma Doma a Jihar Nassarawa bayan tsegunta mu su da aka yi cewa wasu ‘yan-bindiga na shirin kai hari inda aka samu wasu bindigogi kirar gida a tare da su.
A Jihar Benue kuwa sun kai samamen a kananan hukumomin Gwer ta yamma da Logo da kuma Guma, ta hanyar amfani da Jirgi mai saukar Ungulu inda suka samu nasarar kashe tarin ‘yan-bindiga.
Yayin da kuma a Jihar Taraba dakarun tsaron suka farwa yankunan Kwesati da Manya-Garagun inda suka samu nasarar cafke wasu tsageru 8 da bindigogi biyu kirar AK47 da wata karama kirar K2, sai kuma wasu bindigogi biyu kirar gida.
Tuni kuma suka mika wadanda aka kama din hannun jami’an tsaron sirri na DSS don tsaurara bincike.