Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ya zama wajibi shugaba Buhari ya kawo karshen cin zarafin Musulmi- Kungiya

Published

on

 

Gidauniyar mata Musulmi ta Kano ,ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran jami’an tsaron kasar nan suyi gaggawar kawo karshen cin zarafin ‘yan uwa Musulmai a yankin Arewacin kasar nan ,musammman satar yaran musulmi da sauya musu addini zuwa kiristoci.

Sakatariyar Gidauniyar Hajiya Fatima Ibrahim Ilyasu Dorayi ce tayi kiran  a wani taron manema labarai da gidauniyar ta gudanar kan  cin zarafin da ake yiwa Musulmai a Arewacin Najeria.

Hajiya Fatima ta yi Allah wadarai kan yadda aka gano wani Kirista mai suna Solomon ya sato ‘yan gudun hijira na Boko Haram sama da dubu hudu da boye su a gidan sa, yana azabtar dasu tare da yiwa mata fyade wanda tace hakan tamkar tozarta Musulunci ne.

Sakatariyar Gidauniyar Fatima Dorayi ta kara da cewa irin wadannan abubuwa da ake yiwa Musulmi musamman a Arewaci da sauran gurare na tozartawa kamata yayi , ya zama darasi akan Musulmi wajen komawa ga Allah domin samun makoma mai kyau.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito Gidauniyar na kira ga Gwamnan Kano da Masarautar Kano da sauran mahukunta suyi kokarin daukar matakin shari’a kan duk masu kokarin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!