Kiwon Lafiya
Rundunar sojin kasar nan ta kai samage ofishin jaridar Daily trust da ke Maiduguri
Rundunar sojin kasar nan ta ce ta kai samame ofisoshin jaridar jaridar Daily Trust da ke Maiduguri da Abuja ne da nufin gayyatar ‘yan jaridun kamfanin wadanda ke da alhakin ruwaito wani labari da ya fallasa dabaru da kuma tsare-tsaren ayyukan dakarun operation lafiya dole a jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar burgediya janar Sani Usman Kuka Sheka ne ya bayyana haka ga manema labarai ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya.
A cewar sanarwar fallasa dabaru da kuma tsare-tsaren ayyukan soji laifine babba da ke barazanar ga tsaron kasar nan.
Sanarawar ta kuma ce sojojin sun je ofishin jaridar ne da nufin gayyatar ‘yan jaridar da suka ruwaito labarin.
Burgediya janar Sani Usman Kuka Sheka ya kuma ce, rundunar za ta ci gaba da bincike kuma duk wadanda aka samu suna da hannu wajen fitar da bayanai na sojin za a dauki tsastsauran mataki a kansu.
A jiya lahadi ne dai jaridar Daily Trust ta wallafa wani labari kan shirye-shiryen da dakarun operation lafiya dole ke yi na kakkabe mayakan Boko-haram daga yankin Baga da wasu yankuna da ke makwabtaka da wajen.