Kiwon Lafiya
Rundunar sojin kasar nan ta sanar da ‘yantar da fiye da mutane dubu goma
Rundunar Sojin kasar nan ta sanar da cewa ta ‘yantar da fiye da mutane dubu guda daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayar a jiya Litinin, inda ya ce dakarunsu na shiyya ta 22 tare da hadin giwar rundunar Lafiya Dole suka samu nasarar ceto mutanen.
Sannan ya kuma ce sun samu hadin kan dakarun tsaro na kasa-da-kasa na Multintional Joint Task Force yayin aikin.
Janar Texas Chukwu ya kara da cewa an ceto mutanen daga kauyukan Malamkari da Amchaka da Walasa da kuma Gora, dukkansu cikin karamar hukumar Bama a Jihar Borno.
Mafi-akasarinsu dai mata ne da kananan yara tare kuma da wasu matasa da aka tilastawa shiga kungiyar ta Boko Haram.
Birgediya Janar Texas Chukwu ya nanata kudurin rundunar Sojin kasar nan wajen kakkabe duk wani nau’I na ta’addanci a yankin na Arewa Maso Gabas da ma kasa baki-daya, tare da ceto mutanen da ke hannun mayakan.