Kiwon Lafiya
Rundunar sojin Najeriya ta kashe mayakan Boko-Haram bakwai a Sambisa
Rundunar sojin kasar nan ta ce ta kashe wasu mayakan Boko-Haram guda bakwai a maboyar su da ke dajin Sambisa.
Mai magana da yawun rundunar Burgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Ya ce wasu sojoji biyu sun samu raunuka yayin harin kuma tuni aka garzaya da su zuwa asibiti domin kula da lafiyar su.
A cewar Burgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka sojojin sun kuma samu nasarar lalata maboyar ‘yan Boko-Haram da dama da kuma lalata wasu bama-bamai.
Ya kuma ce rundunar sojin sama na kasar nan ta yi ta kaiwan hare-hare ta sama da jiragen ta na yaki domin taimaka wa dakarun da ke kasa wajen fatattakar mayakan na Boko-Haram.