Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta 23 a harin Metele
Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da mutuwar sojojin ta 23 inda kuma wasu 31 suka samu raunuka bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari a sansanin su da ke Metele a ranar 18 ga watan Nuwambar nan da muke ciki.
Sai dai wannan adadi ya saba da adadin da rahotannin suka bayyana a baya cewa ana zargin mayakan sun kashe sojin daga 44 zuwa dari ne.
Cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Usman ya fitar a madadin babban hafsan sojin kasar nan Laftanal Janar Tukur Buratai ta ce a tsakanin 2 ga watan Nuwamba zuwa 17 ga watan, yan Boko Haram sun kai hari kan sojin kasar nan a kauyukan Kukawa da Ngoshe da Kareto da kuma Gajiram.
Ya kuma ce dukkanin hare-haren, rundunar sojin ta kawar da su, sai dai an kashe sojoji goma sha shida inda kuma 12 suka samu raunuka, yayin dauki ba dadin.
Ta cikin sanarwar Sani Usman ya ce al’amarin da ya faru a ranar 18 ga watan, ya faru ne a dai-dai lokacin da rundunar sojin kasar nan ke tsaka da shirye-shiryen babban taron hafsan sojojin kasar nan da aka tsara gudanarwa a garin Benin na jihar Edo.