Labarai
‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun kama mutane 2 da zargin sace wani jariri

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 2 da ake zargin da sace wani jariri mai shekara 1 da rabi a babban asibitin Babura.
A sanarwar da Mai magana da yawon Rundunar, SP Lawan Shisu Adam, ya fitar a jiya ranar Alhamis.
Ya ce, Sanarwar ta ce binciken ya fara ne bayan asibitin ya kai rahoton ɓacewar jaririn daga sashen kula da yara.
Sanarwar, bayan bincike ‘yan sanda sun kama wata mata mai suna Khadija Aliyu tare da jaririn.
Haka kuma, binciken ya kai ga kama wani jami’in jinya, Sadik Sale Yahaya, wanda ake zargin ya haɗa baki da ita wajen aikata laifin.
Ya ce yayin binciken, wacce ake zargin ta bayyana cewa ta kai jaririn zuwa wani gidan marayu a Jihar Kaduna da nufin sayar da shi kan kuɗi Naira ₦2,000,000.
Rundunar ta ce an tsare waɗanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin, sannan za a haɗa jaririn da iyalansa bayan kammala matakan da suka dace.
You must be logged in to post a comment Login