Labarai
Rundunar Sojin Ruwa ta nesanta kanta da labarin sojojin Chadi na sayar da makaman su idan ba su da kuɗi.
Rundunar Sojin Ruwa ta ƙasar nan ta nesanta kan ta da Kwamando Jamila Abubakar, jami’ar da ta zargi sojojin kasar Chadi da sayar da makamansu idan suka shiga matsalar kudi.
Jamila dai ta yi zargin ne yayin taron jin ra’ayin jama’a da kwamitin tsaro na majalisar wakilai da ya shirya a Abuja.
Ta dai zargi yadda sojojin kasar ke sakin makamansu ba bisa ka’ida ba da cewa shi ne ummul-aba’isun kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.
To sai dai a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Suleiman Dahun, ya fitar a ranar Talata, rundunar ta ce ba da yawaunta jami’ar ta furta kalaman ba.
“Rundunar mu na nesanta kanta da ra’ayin wannan jami’ar, muna jinjina wa gudunmawar da makwabtan kasashe suke bayarwa wajen yaki da yaduwar kanana da matsakaitan makamai,” inji sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login