Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Civil Defense ta nesanta kanta daga karbar cin hanci a hannun masu gidajen Mai

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta nesanta kanta da wasu jami’ai da ake alakanta rundunar da su wadanda ake zargin suna karbar cin hanci a daga hannun masu gidajen siyar da man fetur da masu dillancinsa.

hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar da yammacin jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce ko kadan ba jami’an rundunar Civil Defense ne ke karbar cin hanci ba kamar yadda aka ankarar da rundunar akan abinda ke faruwa.

DSC Ibrahim ya kuma ce, ”Babu inda Civil Defense ta Kano ta tura jami’anta gurin masu gidajen sayar da man fetur da masu dillancinsa domin su karbi cin hanci da rashawa daga wajen su”

Haka kuma, sanarwar ta ce, yanzu haka kwamandan rundunar Adamu Idris Zakari, yabada umarnin kuma an fara gudanar da bincike domin  bankado masu aikata irin wannan cin amana domin daukar matakin shari’a a kansu.

Rundunar ta yi kira ga mutane da su gaggauta kai mata rahoton masu irin wannan dabi’a.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!