Connect with us

Labarai

Rundunar sojin saman ƙasar nan za ta sauya tsarin biyan fanshon ma’aikatan ta

Published

on

Rundunar sojin saman kasar nan ta ce ta kammala tsare-tsaren da suka kamata na sauya tsarin biyan fanshon ma’aikatanta zuwa na zamani.

Shugaban hukumar fansho na rundunar Air kwamado Saburi Lawal ne ya bayyana hakan a Abuja.

Komodo Saburi ya ce sauya tsarin zuwa na internet zai fara aiki nan da karshen shekara da zarar an samun izini daga hukumomin da suka dace.

Ya ce a yanzu rundunar na amfani da tsarin biyan fansho na kafa da kafa zuwa jihohin kasar nan.

A don haka ya ce rundunar za ta koma amfani da tsarin biyan fanshon ta hanyar Internet.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!