Labarai
Rundunar Civil Defence za ta baza jami’ai 1,350 yayin bukukuwan kirsimeti a jihar Kano

Rundunar tsaron Civil Defence a jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a fadin jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da freedom radio.
Ya ce rundunar za ta fitar da jami’ai 1,350, domin tsaron wuraren ibada, kasuwanni, da wuraren shakatawa a duk fadin jihar, domin tabbatar da komai na tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba.
Rundunar ta Civil Defence ta kuma bukaci ƙarin haɗin kai daga al’umma, domin dakile ayyukan masu barnata kayan gwamnati da ma kadarorin da aka samar don cigaban ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login