Kiwon Lafiya
Rundunar yan sanda a Akwa Ibom sun kame ma’aikatan sa idon aikin zabe na boge
Rundunar ‘yan’sanda jihar Akwa Ibom ta ce ta samu nasarar cafke mutane goma da suka kashe wani mutum tare da kona motoci goma sha daya a kusa da ofishin hukumar zabe ta kasa da ke Uyo babban birnin jihar.
Haka kuma kwamishinan ‘yan’sandan jihar Bashir Makama, ya ce, sun kama wasu mutane da katunan zabe na dindindin da adadinsu ya kai dari da saba’in da tara, sai kuma katin zabe na wucin gadi guda ashirin da bakwai.
Ya ce, yayin samamen sun kama mutane arba’in da daya da suka ce su masu sanya ido ne, sai dai babu wata hujja da ta tabatar da hakan.
Da yake ganawa da manema labarai jiya a garin Uyo Bashir Makama, wanda ya samu wakilcin jami’in yada labaran rundunar ‘yan’sanda jihar ta Akwa Ibom DSP Odiko Ogebeche, ya ce, sun kuma samu nasarar kashe wutar da wadannan bata gari suka kunna.
Sai dai DSP Odiko Ogebece ya musanta cewa rundunar ta kama ‘yan bangan siyasa guda dari hudu da ake cewa sun kama, sai dai ya ce, sun kama mutane goma kuma kawo yanzu babu wanda suka samu yana alaka da wata jam’iyya.